Alaramma Sanusi Bauchi a cikin nasihar watan Ramadan ya bayyana cewar a wannan wata ana bukatar kowa ya sa wa kansa natsuwa, ya sa wa kansa tsoron Allah, kuma ya yi kokarin zama lafiya da kowa, kuma ya kauce ma duk wani abin da zai sa ya sabawa Allah.
A wajan koya zama lafiya a irin wannan watan, mazon Allah (SAW) cewa ya yi idan dayan ku ya wayi gari yana azumi har aka sami wani yazo ya tsokane shi, ko ya zage shi ko kuma ya nemi fada da shi, to kada ya biye ma wanda ya neme shi da tsokana, kamata ya yi ya ce ni mutum ne mai azumi.
Dan haka kowa ya yi kokari kar ya tsokani wani, kar ya takali wani ko ya zagi wani. Kaga cewar wato idan ana azumi ba’a tada hankali ko fitina, kowa ya yi kokarin zama lafiya da kansa da kuma sauran bayin Allah.
Zaman lafiyan nan idan babu shi ko ba a watan azumi kadai ba, a ko yaushe ibada bata yiwuwa, idan babu zaman lafiya. Babu maganar neman arziki ko shugabanci nigari ko mai mulki ya mulki talakawa, babu abinda ke yiwuwa idan babu zaman lafiya, dan haka ubangiji Allah ya bamu zaman lafiya.
Saurari Nasihar Anan