Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alamu Shafin Aika Takardun Daukar Malamai 500,000 Ya Fara Da Tangarda


Da alamu shirin nan na gwamnatin tarayyar Najeriya na daukar malaman makaranta dubu dari biyar 500,000 da gwamnatin kasar ta bada sanarwar zai fara aiki ranar 12 ga wannan wata na Yuni ya fara da tangarda a sakamakon daina aiki da shafin aikawa da takardun neman aikin na yanar gizo ya yi wanda ake zargin cewa yawan jama’ar da suka nemi shiga shafinne ya haifar da matsalar.

Satin da ya gabata ne gwamnatin tarayyar kasar ta fitar da sanarwar daukar malaman makaranta har guda dubu dari biyar a fadin kasar kuma a cewar ta za’a fara karbar takardun neman aikinne a ranar lahadi 12, ga watan Yuni, kuma ta ce duk wadanda suke da shi’awar aikin su aika da takardun su a shafin yanar gizon da ta samar na musamman mai adireshi http//portal.npower.gov.ng.

Amma kamar yadda mujallar Punch ta wallafa, wani daga cikin wakilin su yayi kokarin ziyartar wannan shafi da misalign karfe 6:48pm na yamma a ranar da shafin ya kamata ya fara aiki amma bashi ba alamar sa a yanar gizon, binciken ya nuna alamun cewa shafin ya sami tangarda ne a sakamakon yawan jama’ar da suke kokarin aika takardun nemen aikin.

Mai ba ministan ilimi shawara na musamman Mr Anthony Akume, a yayin da aka nemi jin ta bakinsa akan yawan takardun nemen aikin da jama’a suka fara aikawa kawo yanzu, ya bayyana cewa baza a iya ganewa ba a yanzu haka.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG