Nasarawa: Masu Kananan Sana'o'i Sun Yaba Da Tallafin Gwamnatin Tarayya

Kusan shekara biyu kenan da gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da wani shiri na bada tallafin kudi ga masu karamin karfi a jihar Nasarawa.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana daga tallafin na gwamnatin tarayya don inganta sana’oinsu a jihar Nasarawa sun yaba da matakin, sun kuma yi alkawarin yin amfani da kudin wajen habbaka tattalin arzikinsu.

Shirin bada tallafin na gwamnatin tarayya a karkashin shugaba Muhammadu Buhari, an yi shi ne musamman don taimakawa marasa galihu.

Jami’in dake kula da shirin gwamnatin tarayya na inganta rayuwar jama’a a jihar Nasarawa, Imran Usman Jibrin, ya ce mutane fiye da dubu arba’in da takwas a kananan hukumomi shida na jihar ne zasu ci moriyar shirin.

Sana'ar hannu

Shugaban karamar hukumar Lafia, Mu’azu Aminu Maifata, ya ce tallafin zai rage radadin talauci a tsakanin al'umma. Ya kuma ce tallafin ya taimaka wajen rage yawon maula a jihar.

Saurari karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Nasarawa: Masu Kananan Sana'o'i Sun Yaba Da Tallafin Gwamnatin Tarayya