Kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi ta fada a jiya Juma’a cewa ta tambayi wani babban jam’in soja a ma’aikatar tsaro ta Pentagon game da matakan da za a iya dauka na hana shugaban kai harin nukiliya.
Tunanin yiwuwar hakan ka iya faruwa ne yasa Pelosi da wasu shugabanni a kasar suka fara tunanin tsige Trump daga mulki duk da cewar sauransa ‘yan kwanaki kalilan ya gama wa’adinsa ranar 20 ga watan Janairu.
Ta ce “ da wannan safiya na yi magana da shugaban hadin gwiwa na kwamitin manyan hafsoshi Mark Milley inda muka tattauna a kan hanyoyin takawa shugaban mara tabbas burki daga daukar matakan soja da samun lambar nukiliya da kuma damar bada umarnin kai harin makaman nukiliya” Pelosi ta rubuta a wata wasikar da ta aikewa ‘yan uwanta ‘yan Democrat a majalisar wakilai.
A wani yunkurin tabbatar da wannan hirar, mai magana da yawun Milley ya tabbatarwa Murray Amurka cewa, “Ya amsa mata tambayoyi da ta yi masa a kan samun izinin lambar nukiliyar.”
Sai dai mai magana da yawun Milley bai yi wani karin bayani mai zurfi ba yayin kirar.
Da yammacin jiya Juma’a ne kafar labarai ta NBC ta fada cewa Pelosi da fadawa ‘yan uwanta na Democrat cewa an bata tabbaci akwai matakan kariya da zasu hana Trump duk wani yunkurin bada umarnin kai harin nukiliya.
Karin bayani akan: Donald Trump, Joe Biden, Muryar Amurka, da Nancy Pelosi