Nan Gaba Will Smith Zai Bukaci Kulawa Saboda Yana Tsufa – Jada Pinkett

Will, hagu, da Jada, dama (Tsohon hoto)

A wannan makon fitacciyar jarumar ta fasa kwan cewa ita da Will sun rabu tun a shekarar 2016, amma ba su fadawa duniya ba.

Fitacciyar ‘yar wasan kwaikwayo a Amurka Jada Pinkett Smith, ta ce Will Smith zai bukaci wanda zai kula da shi a nan gaba, saboda tsufa na riskar shi.

Ta bayyana hakan ne yayin wata hira da ta yi da jaridar The Times.

A wannan makon fitacciyar jarumar ta fasa kwan cewa ita da Will sun rabu tun a shekarar 2016, amma ba su fadawa duniya ba.

Hakan na nufin ma’auratan sun kwashe shekaru bakwai suna basajan cew su ma’aurata ne.

A shekarar 1997 Will da Jada suka yi aure, suna kuma da ‘ya’ya biyu, Jaden mai shekaru 25 da Willow mai shekaru 22.

Will yana da wani da mai suna Trey a aurensa na farko.

Jada ta fada a hirar cewa rabuwar ta su an yi ta ne ba tare da shiga kotu ba, inda ta kwatanta lamarin a matsayin rabuwar aure ba tare da an sanya hannu a takardu ba.

Amma yayin hirarsu The Times, Jada ta ce mai yiwuwa nan gaba, za su sake komawa a matsayin miji da mata ko don ta kula da shi saboda ya fara tsufa.

A halin yanzu Jada mai shekaru 52 na zama ne a wani gida da ba shi da nisa da gidan Will mai shekaru 55.