Kwararre a ilimin kimiyya da fasaha a Najeriya, Dr. Grema Kyari ya ce nan da shekara ta 2030 rabin ayyukan duniya za su koma kan na'urori, wanda hakan zai rage dogaro ga aikin karfi.
Kyari ya ce hakan a lokaci guda na nuna damar samun ayyuka cikin sauki bisa kwarewa a fannin fasaha.
Ya kara da cewa wannan farkarwa ne ga wadanda ke kammala makaranta da korafin ba ayyukan yi su dage wajen koyon fasahar sana'a da ke kan na'ura mai kwakwalwa.
Kyari ya ce daga ko’ina mutum ya ke rayuwa zai iya samun aikin yi da zai ba shi albashi ko kudin shiga don kula da tsadar rayuwa.
Kalaman na Kyari na zuwa ne yayin da wta tawagar kwararru suka zaga sassan Najeriya musamman yankunan karkarar arewa don wayar da kan matasa kan wannan abun da ke tinkarowa nan da shekaru 6 masu zuwa.
Shi kuma babban sakatare a ma'aikatar kasuwanci da masana'antu Ambasada Nura Abba Rimi ya ce 'yan Najeriya na ci gaba da samun kwararru da kan yi fice a duniya kuma gwamnati na ba su kwarin gwiwa.
Karancin wutar lantarki, rashin wayar da kai da tsadar kayan aiki na daga cikin dalilan da kan kawo rashin amfanar dalibai da ma sauran 'yan Najeriya masu karamin karfi wajen cin moriyar fasahar zamani a cewar kwararru.
Saurari cikakken rahoton Hauwa Umar daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5