Nakasassu Sun Koka Da Rashin La’akari Da Su a Batun Rajistar Dan Kasa

Nakasassu

Duk da matakan da hukumomin Najeriya su ka ce su na daukawa don saukaka ma nakasassu rayuwa, har yanzu nakasassun na zargin hukumomin kasar da rashin kula su.

Masu fama da matsalar nakasa a Najeriya sun koka dangane da rashin basu kulawa kamar yadda ya kamata, musamman a kokarin ganin su ma sun samu damar yin rejista ta sabunta katunansu na shaidar zama dan kasa don kar a rufe layukansu na wayar salula musamman kamar yanda doka ta tanada.

kawo yanzu dai miliyoyin ‘yan Najeriya ba su samu damar yin rajistan ba. Yayin da ma’aikata a hukumar neman shaida ta kasa a Najeriya NIMC a takaice suka dawo daga yajin aikin da suka shiga sakamokon koken rashin biyansu hakkokinsu, masu fama da nakasa a kasar su bayyana damuwarsu dangane da matsalolin da suke fuskanta a kokarin ganin su ma sun samu rajistar sabunta katinsu na zama dan kasa don kar a rufe musu layukansu na wayar salula.

ABUJA: Halin da nakasassu ke ciki a Nigeria

Kimanin nakasassu ko masu bukata ta musamman miliyan 17 ne ke fuskantar barazanar rufe layukansu na salula, saboda kasa samun damar sabunta katunansu na dan kasa. Lamarin da Alhaji Musbahu Lawan Didi, shugaban masu lalurar cutar shan inna, wato polio a turance, ya danganta da rashin aiwatar da wani tsari da zai tallafa wa masu bukatu ta musamman a cikin wannan shiri

A shekarar 2018, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu akan dokar da ta umarci ma’aikatu da sauran wuraren da suka shafi huldar jama’a, da a ba su damar aiwatar da bukatunsu ba tare da sun bi layi ba. To ko me ya sa ba a basu irin wannan dama a wasu ofisoshin gwamnati?

Malam Shehu Garba shi ne mai baiwa shugaban Najeriya shawara a kan harkokin mutane masu bukata ta musamman, ya ce dayake ba a dade da sanya ma dokar hannu ba, fadakarwa ba ta wadata ba. Don haka ana ta cigaba da fadakarwa ga wadanda abin ya shafa da kuma masu ruwa da tsaki.

Masannin shari’a barista Umar Mainasara Kogo ya yi kari da cewar da bukatar a rika la’akari da nakasassu a duk lokacin da ake wani muhimmin al’amari. Ya ce akwai dokoki da dama da aka kafa don ganin an yi adalci ma rukunonin marasa karfi.

Ga Shamsiyya Hamza Ibrahin da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Nakasassu Sun Koka Da Rashin La’akari Da Su a Batun Rajistar Dan Kasa