Yarima Suleiman Ibrahim da ya jagoranci nakasassun ya bayyana cewa an kama wasu daga cikinsu da ke bara a cikin Abuja a makon da ya gabata inda aka bayar da belin su uku akan Naira dubu arba'in da biyar. Yana mai cewa idan ba a basu damar bara ba a ina zasu samo kudin biyan beli?
Sarkin kutare Ali Isa Sarkin Kutare Abuja, ya ce da su aka yi gwagwarmaya a zaben 2015 amma har yanzu ba gani a kasa ba.
A bangaren mata, shugabarsu Fatima Suleiman ta ce ta iya sana'ar hannu kamar hada omo da sabulan da sauran wasu abubuwa amma ba ta da jari shi yasa take fita yin bara
Shugaban nakassun Yarima Suleiman ya ce idan gwamnatin tarayya na son su yi tafiya tare da ita, to lallai ta zauna da su a duba matsalolin da ke sa su yin bara domin a gyara.
Sai dai minista mai kula harkokin matasa, Barista Solomon Dalung ya ce akwai matakan da gwamnati ke dauka.
Yace "Idan gida ya lalace, gyaranta ba zai yiwu a gama a rana guda ba,"
Majalisar Dokokin Najeriya na shirin yin doka ta za ta bai wa nakassun kashi 20 cikin 100 na dukkanin mukamai.
Your browser doesn’t support HTML5