NAKASA BA KASAWA BA: Yadda Wani Matashi Mai Tawaya a Kafafu Ke Fafitikar Nemar Wa Kansa Abin Dogaro - Yuli 14, 2022

Souley Mummuni Barma

A makon jiya shirin ya samu bakuncin Aboubakar Ali wani dalibi dake karantar fannin Accounter kokuma Comptablite a wata makarantar biya dake Damagaram a Jamhuriyar Nijer yayinda a daya bangare ya ke ci gaba da tallar kayan miya don samun abin biyan bukatun yau da kullum. Matashin wanda Allah ya jarabce shi da tawaya a kafa ya fara karatunsa ne a wata makarantar nakasassu a matakin framari , sanin mahimmancin ilimi ya sa Aboubakar dagewa da neman hanyoyin ci gaba da karatu ta yadda wata rana zai hucewa kansa takaici.

Saurari karashen hirarsu da wakiliyar sashen hausa Tamar Abari:

Your browser doesn’t support HTML5

NAKASA BA KASAWA BA: Yadda Wani Matashi Mai Tawaya a Kafafu Ke Fafitikar Nemar Wa Kansa Abin Dogaro