NAKASA BA KASAWA BA: Yadda Wani Mai Kirar Karafan Kyalkyali Na Mata Ya Yi Fice - Satumba 14, 2023

Souley Mummuni Barma

To har yanzu muna jihar Agadez da ke yankin arewacin Jamhuriyar Nijar inda masu bukata ta musamman ke fafutukar neman na kai da nufin ba da gudunmowa a ayyukan ci gaban al’umma.

Oughoumour Ahmoudou wani mai kirar kayayakin azurfa da sauran karafan kyalkyali na adon mata da suka hada da sarka da dan kunne da zobe da dai sauransu ya yi fice a wannan fanni lamarin da ya ba shi damar samun kyaukyawar mu’amula da jama’a na ciki da wajen wannan kasa.

Bakon shirin wanda a baya ya yi bayani kan irin alherin da ya samu ta hanyar sana’a ya lakanci aikin kera makullan mota.

To sai dai duk da haka a na fuskantar kalubale kamar yadda ya bayyana a ci gaban hirarsa da wakilin sahen hausa Hamid Mahmoud.

Saurari shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

NAKASA BA KASAWA BA