NAKASA BA KASAWA BA: Yadda Masu Bukata Ta Musamman A Najeriya Ke Ba Da Gudummawa Wajen Ci Gaban Al’umma, Kashi Na Biyu – Disamba 14, 2023

Souley Mummuni Barma

Shirin Nakasa Ba Kasawa na wannan makon, zai kawo muku ci gaban tattaunawar da wakiliyarmu Medina Dauda ta yi da daya daga cikin shugabanin kungiyoyin nakasassun arewacin Najeriya, Yarima Suleiman Ibrahim, mai laurar makanta da ke bincike a kan zamantakewar al’umma musamman abin da ya shafi sha’anin tsaro.

Yarima ya nuna damuwa kan yadda a wasu jihohin Najeriya hukumomi ke farautar masu bukata ta musamman da suka rungumi bara a sakamakon rashin madogara.

To amma za mu dora daga inda yake bayani game da irin gudunmowar da nakasassu ke iya bayarwa wajen magance matsalolin tsaro.

Saurari shirin cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

NAKASA BA KASAWA BA: Yadda Masu Bukata Ta Musamman A Najeriya Ke Ba Da Gudummawa Wajen Ci Gaban Al’umma 6'00".mp3