NAKASA BA KASAWA BA: Waiwaya Maganin Mantuwa, Tattaunawa Da Madame Boukari , Disamba, 22, 2022

Souley Mummuni Barma

A farkon watan Mayun da ya gabata kungiyoyin nakasassu daga sassan Jamhuriyar Nijer su ka ci kasuwar baje koli a birnin Yamai inda suka je da kayayakin kere -keren sana’oin hannu da nufin gwada wa al’ummar ciki da wajen wannan kasa irin basirar da Allah ya yi wa masu bukata ta musamman. Sai dai duk da kiraye -kirayen da aka sha yi akan bukatar baiwa nakasassun goyon bayan da zai kara masu azama a ayyukan da suka sa gaba a matsayin wani bangare na matakan yaki da bara, da alama al'umma ba ta fahimci mahimmancin gudunmuwar da ake fatan samu daga gareta ba kamar yadda shugabar kwamitin tsare -tsaren Madame Boukari Kadidja Amadou ta shaida wa wannan shiri.

Saurari cikakken shirin cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

NAKASA BA KASAWA BA: Tattaunawa da Madame Boukari