NIAMEY, NIGER - A shirin Nakasa Ba Kasawa Ba na wannan makon za mu ci gaba ne da takaitaccen tarihin Dalhat Sabi’u Mohammed shugaban wata makarantar islamiya a Kaduna, wanda ke da tawaya a dukkan kafafunsa biyu.
Mutum ne da ke sha’awar karatu, saboda haka a zamanin da yake matashi ya hada boko da karantun islamiya kamar yadda ya ‘dan taba wasu sana’oi kamar aikin nika, a matsayin wata hanyar samin abin rufin asiri.
Saurari cikakken shirin da Souley Moumouni Barma ya gabatar:
Your browser doesn’t support HTML5