NAKASA BA KASAWA BA: Kungiyoyin Nakasassu A Najeriya Na Ci Gaba Da Bitar Babban Zaben Kasar, Maris 16, 2023

Souley Mummuni Barma

Kasancewar a wannan makon za a gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalissar jiha ya sa shirin na yau ke kara maida hankali kan zabukan domin jin korafe-korafen masu bukata ta musamman don ganin an magance matsalolin da suka fuskanta a baya. Abdurahaman Usman Muhammed, da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano, ya yi wa shirin nakasa bayani dangane da yadda abubuwa suka wakana a shiyyarsa.

Abdurahaman ya kuma bayyana fatan ganin an yi amfani da damar zaben ranar 18 ga watan Maris don tantance girma ko kuma nauyin kuri’un nakasassu. A cewarsa wannan na iya zama wani matakin ankarar da ‘yan takara matsayinsu a harkar zabe.

Saurari cikakken shirin cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

NAKASA BA KASAWA BA: Kungiyoyin Nakasassu A Najeriya Na Ci Gaba Da Bitar Babban Zaben Najeriya