Wannan yunkuri dai wani bangare ne na fafutukar ganin mutanen da ke tawaya sun mori ‘yancin da ke kunshe cikin yarjeniyoyin da kasashe suka cimma da Majalisar Dinkin Duniya.
niamey, niger —
Batun ilimin nakasassu da samar da ayyukan yi shi ne makasudun bullo da wannan shiri wanda a dayan gefen ke hangen fadakar da iyaye muhimmancin bai wa yara nakasassu kulawa ta musamman.
Daraktan makarantar makafi Ecole Soly Abdourahamane, da Malan Moussa Nasser, sun bukaci hadin kan al’umma domin cimma gurin da aka sa gaba a karkashin wannan shiri da za a aiwatar a tsawon watanni 12.
Daraktan ya ce yana fata kamar yadda aka yi a Tahoua, matasa na yankin Yamai zasu natsu domin daukar darussan da za a karantar da su a yayin wannan horo game da abubuwan da ke kunshe cikin kundin hakkokin nakasassu.
Saurari cikakken shirin cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5