Shirin Nakasa Ba Kasawa Ba na wannan makon ya sami bakuncin wani dan asalin jihar Adamawa da ke zaune a jihar Enugu a yankin kudu maso gabashin Najeriya.
niamey, niger —
Bakon shirin wanda ya tsinci kansa cikin halin tawaya bayan da ya yi fama da rashin lafiya a lokacin yarinta, bakanike ne da ya yi fice a garin Enugu wajen gyaran keke NAPEP da aka fi sani da adaidaita sahu.
Malan Sa’idu Ali, na alfahari da baiwar da Allah ya yi masa, dalili kenan ya rungumi sana’arsa a matsayin madogarar rayuwa.
A hirarsa da wakilin Muryar Amurka Alphonsus Okoroigwe, Malam Sa’idu ya fara da yin bayani game da ainahin yadda aka yi ya shiga halin Nakasa.
Saurari cikakken shirin da Souley Moumouni Barma ya gabatar:
Your browser doesn’t support HTML5