NAKASA BA KASAWA BA: Darasi Daga Matar Da Ta Rungumi Kaddara, Nuwamba 09, 2023

Souley Mummuni Barma

NIAMEY, NIGER - A shirin Nakasa Ba Kasawa Ba na wannan makon za mu yi bankwana da Hajiya Ai’sha ‘Yar Gata” mawakiya kuma mai zane-zane da ke garin Tema na kasar Ghana, wacce ta tsinci kanta cikin halin tawaya sanadiyar hatsarin mota ba ta bari wannan al’amari ya katse mata hamzari ba. Abin da ke nufin a rayuwa komai na iya faruwa kamar yadda ‘yan magana ke cewa matsawar ba a mutu ba halitta ba ta kare ba.

Saurari cikakken shirin da Souley Moumouni Barma ya gabatar:

Your browser doesn’t support HTML5

NAKASA BA KASAWA BA: Darasi Daga Matar Da Ta Rungumi Kaddara A Harkokinta Bayan Hatsari, Nuwamba 09, 2023.mp3