NIAMEY, NIGER —
A makon da ya gabata shirin ya tattauna da Steven GYAN shugaban kungiyar nakasassun yankin Ashanti a Ghana, wanda a kashin farko na tattaunawarsu da wakilin muryar Amurka Hamza Adam ya koka a game da kyamar da masu bukata ta musamman ke fuskanta daga wasu daidaikun mutane a sahun al’umma, alhali kasar na daga cikin wadanda suka yi na’am da yarjeniyoyin kasa da kasa kan mutunta ‘yancin nakasassu.
Wannan na wakana ne a wani lokaci da kudaden tallafin masu bukata ta musamman suka makalle a hannu mahukunta, abin da ke shafar dukkan lamuran rayuwarsu.
Saurari ci gaban shirin:
Your browser doesn’t support HTML5