Najeriya Za Ta Gina Gadar Ibbi Da Ta Hada Taraba Da Filato

Irin gadar da za'a gina

Yanzu haka al’ummomin jihar Taraba sun soma murna game da batun gina wata gada a babban kogin Ibbi da ya shiga babban kogin Benue da ya hada jihar da jihar Filato, aikin da aka dau fiye da shekaru 30 ana cacar baki akan yin shi.

Fiye da shekaru 30 ke nan ake maganar gina gadar Ibbi , da ta hada jihar Taraba da Filato wadda ka iya tada komadar tattalin arzikin al’ummomin Ibbi da Wukari dama sauran yankunan da suke ke kan iyakan jihohin biyu.

Tun ba yau ba ne al’ummomin yankin Ibbi da Wukari ke kokawa game rashin babbar gada da ta ratsa wannan kogi na Ibbi wanda ke cikin manyan kogunan da suka shiga babban kogin Binuwai a Najeriya.

Mallam Abdulhamidu Mahmuda Ali Yara,dan asalin yankin Ibbi,ya bayyana farin cikinsu game da tado da aikin gadan kogin Ibbin da gwamnatin tarayya ta yi a yanzu,musamman a wannan lokaci da ba kasafai ake samun manyan jiragen ruwa dake ketara kogin Binuwai ba. Yace can baya, tsohon shugaba Yakubu Gowon ya yi alkawarin gina gadar amma cikin shekara daya aka hambar da gwamnatinsa. Haka shima tsohon shugaba Obasanjo ya yi alkawain gina gadar, amma hakansu bata cimma ruwa ba.

Gwamnatin tarayya ta riga ta baiwa kamfanin RCC kwangilar gina gadar

Batun aikin madatsar Mambilla, da Kogin Ibbi da kuma na Karim Lamido na cikin alkawuran da shugaba Buhari yayi lokacinda yake yakin neman zabe a jihar Taraba. Ambassador Hassan Jika Ardo, tsohon shugaban jam’iyar APC a jihar Taraba, wanda yanzu kuma shi ne jakadan Najeriya a kasar Sau Tome, na da tabbacin shugaba Buhari zai cika alkawarin da ya dauka musu.

A saurari karin bayani a rahoton Ibrahim Abdulaziz

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Najeriya Za Ta Gina Gadar Ibbi da Ta Hada Taraba da Plato – 3’ 42”