COVID-19: Najeriya Za Ta Ci Gaba Da Amfani Da Maganin Chloroquine - NAFDAC

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya wato NAFDAC ta jadada cewa, Najeriya za ta ci gaba da yin amfani da maganin Hydroxichloroquine domin warkar da cutar coronavirus, duk da gargadi na dakatar da amfani da maganin na gajeren lokaci domin yin nazari a kai da hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayar.

A ranar talata da ta gabata babban daraktar Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC, Mojisola Adeyeye, ta bayyana cewa, kasar zata ci gaba da jarraba maganin Hydroxychloroquine saboda akwai kwakkwaran binciken da ya nuna cewa maganin na warkar da cutar coronovirus musamman a lokacin da cutar ba ta yi tsanani ba.

Ta kara da cewa, bayanan da hukumar lafiya ta duniya ke amfani da su kan masu dauke da cutar COVID-19 da suka yi amfani da maganin Chloroquine ya sha bamban da na kasar, kuma akwai yiyuwar nan da watanni 3 zuwa 4 za a samu maganin cutar coronavirus duba da yadda likitoci, masana kiwon lafiya, masu maganin gargajiya suka kara kaimi wajen aikin neman magani.

Jagoran kwamitin ko-ta-kwana na gwamnatin tarayyar Najeriya, Dr. Sani Aliyu, ya ce a duk lokacin da aka sami bullar wata cuta, ana gudanar da gwaji a kan duk maganin da aka samar wato “Early Science” a turance, domin tabbatar da cewa ba zai yi illa ga mutane ba idan suka yi amfani da shi.

Dr. Sani Aliyu ya yi kira ga al’umma da su rika neman shawarar likitoci kafin su yi amfani da magani, saboda illar dake tattare da yin amfani da su na tsawon lokaci ba tare da umarnin masana harkar lafiya ba.

Saurari Karin bayani cikin sauti daga Halima Abdulrauf.

Your browser doesn’t support HTML5

COVID-19: Najeriya Za Ta Ci Gaba Da Amfani Da Maganin Chloroquine - NAFDAC