Najeriya: Za A Kafa Tashoshin Zamani Na Motoci

Wasu Karin Jihohi A Najeriya sun amshi zabin ware fili don kafa tashar zamani ta tsayawar manyan motoci don rage hatsari da samun kudin shiga.

Biyo bayan cimma yarjejeniyar da gwamnatin Najeriya ta hukumar shiga yarjejeniya da sassa masu zaman kan su “Concesion Regulatory Commission” kan kafa tashoshin zamani na tsayawar manyan motoci, yanzu an samu karin yankunan Najeriya da su ka aza harsashin kafa tashar.

Irin wadannan tashoshin dai na da tagomashi a kasashe masu ci gaban masana’antu, inda a Najeriya wasu garuruwan kan manyan hanyoyi kan zama a cunkushe da manyan motoci da kan dakata don hutawa da hakan kan toshe manyan hanyoyi.

Misalan biranen da direbobin manyan motocin kan tsaya sun hada da Obolo-Afor a jihar Enugu, Potiskum a jihar Yobe, Tafa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, Marabar Jos da ma Dikko a Neja, inda kwanan nan wata tankar mai ta kama da wuta har a ka samu asarar rayuka.

Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya aza harsashin gina irin wannan tasha a garin Potiskum da kullum akalla manyan motoci 400 ke shiga da fita daga garin.

Shugaban hukumar kasuwanci ta jiragen ruwa, Hassan Bello, da hukumar sa ke jagorantar aikin, ya ce baya ga rage hatsari, tsarin zai samar da tsaro ga kayan da aka yi oda.

Duk da yunkurin dawo da titin dogo, har yanzu kashi 90% na kayan da akan yi oda a raba birane da kauyuka, manyan motoci ke kaiwa.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya- Za a Kafa Sabbin Tashoshin Zamani Na Tsayawar Manyan Motoci