Najeriya vs Benin: Maki Nawa Su Ke Bukata Kafin Samun Gurbi a AFCON?

'Yan wasan Super Eagles bayan da suka kammala atisaye a Legas (Hoto: Instagram)

Najeriya ce ke jagorantar rukunin L da maki takwas sannan Benin na biye da ita da maki bakwai.

‘Yan wasan Super Eagles na Najeriya, na shirin karawa da takwarorinsu na Squirrels of Benin a ci gaba da neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON.

A jiya Juma’a ‘yan wasan na Najeriya suka isa kasar ta Jamhuriyar Benin da ke makwabtaka da Najeriyar, inda suka isa kasar ta kwale-kwale, saboda abin da hukumomin kasar suka ce rashin kyawun hanya.

Najeriya ce ke jagorantar rukunin L da maki takwas sannan Benin din na biye da ita da maki bakwai.

Kungiyoyin biyu za su kara ne a filin wasa na Charles de Gaulle da ke birnin Porto Novo.

Najeriya na bukatar maki daya ne tal ta zamanto ta samu gurbi a gasar wacce Kamaru za ta karbi bakunci a badi.

Kungiyar ta Super Eagles ta gayyaci ‘yan wasa 24 domin buga mata wannan wasa da wanda za ta yi da kasar Leshotho a ranar Talatar mai zuwa a filin wasa na Teslim Balogun da ke Legas.

Kocin Super Eagles Gernot Rohr ya gayyato har da ‘yan wasan gasar Premier ta cikin gida, inda ya sirka su da wadanda ke taka leda a kasashen waje.

‘Yan wasan da aka gayyato sun hada Ahmed Musa, Oghenekaro Etebo, Joseph Ayodele-Aribo, William Ekong, Abdullahi Shehu, Kelechi Iheanacho, Tyronne Ebuehi da Maduko Okoye da dai sauran su.

A halin da ake ciki, Morocco da Ivory Coast sun Samu guraban shiga gasar.

Morocco ta samu gurbinta ne bayan da Burundi da Jamhuriyar Tsakiyar Afrika suka tashi da ci 2-2.

Ita kuwa Ivory Coast ta samu shiga gasar ne bayan da ta lallasa Jamhuriyar Nijar da ci 3-0.