Najeriya Tana Bukukuwan Cika Shekaru 51 Da Samun 'Yanci

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya yana duba fareti lokacin da aka rantsar da shi

Shugaba Goodluck Jonathan yayi jawabi inda yayi alkawarin tabbatar da tsaro a cikin kasar

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya lashi takobin tabbatar da tsaro a kasarsa.

Shugaban na Najeriya yayi wannan alkawarin cikin jawabin da yayi ga kasa yau asabar domin murnar kewayowar ranar samun ‘yancin kai. Mr. Jonathan yayi wannan jawabi nasa a daidai lokacin da aka girka jami’an tsaro masu yawan gaske a Abuja da kuma sassan kasar baki daya.

Ya ce gwamnatinsa tana yin tur da dukkan matakan tashin hankali ya kuma lashi takobin cewa hare-hare na ‘yan kwanakin nan da ake dora laifinsu a kan kungiyar Boko Haram, ba su ne zasu shata makomar kasar ba.

A cikin watan Agusta, wani harin bam da aka ce kungiyar Boko Haram ce ta kai ya kashe mutane 23 a hedkwatar ofishin Majalisar Dinkin Duniya na Najeriya a Abuja.

A lokacin bukukuwan ranar samun ‘yancin da aka yi bara a Abuja, babban birnin na Najeriya, wasu tagwayen bama-baman da aka boye cikin mota sun tashi kusa da inda ake fareti, suka kashe mutane 12. Kungiyar ‘yan tsageran yankin Niger Delta mai suna MEND ta dauki alhakin kai wannan harin.