Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Gawarwakin Mutum 12 A Jahar Rivers Mai Arzikin Man Fetur


Nigerian troops man a checkpoint to prevent sectarian violence.
Nigerian troops man a checkpoint to prevent sectarian violence.

Hukumomin Najeriya sun gano gawarwakin mutane 12 a jahar kasar mai arzikin man fetur

Hukumomin Najeriya sun gano gawarwakin mutane 12 da ba a san ko su waye ba a wani kauyen kudancin kasar.

Jamia'i a jahar Rivers sun fada ranar Jumma'a cewa an gano gawarwakin ne a kauyen Uni Ikata, a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur a kasar Najeriya.

'Yan sandan Najeriya sun ce nan take babu tabbas game da abun da ya janyo mutuwar mutanen, kuma su ka ce babu wasu rahotannin barkewar wasu fadace-fadace kwanan nan a yankin.

Wasu sassan yankin tsakiyar kasar Najeriya sun yi fama kwanan nan da karuwar tashin hankalin addini da na kabilanci.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce daga watan agusta an kashe mutane 70 a fadan da aka gwabza a yankin tsakiyar kasa wanda ke tsakanin kudu da arewa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG