Mukaddashin shugaban hukumar alhazan Najeriya NAHCON Barista Abdullahi Mukhtar ya bukaci shugabannin sassa na hukumar, da su shirya bayanan mika jagoranci ga sabbin shugabannin hukumar.
Wannan ya biyo bayan turawa majalisar dattawa jerin sunaye da za su karbi ragamar shugabancin hukumar karkashin sabon shugaba Zikrullah Olakunle daga jihar Osun da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.
A wani taro da jami'an hukumar kamar yadda jami'ar labaru Fatima Sanda Usara ta sanar, Mukhtar ya bayyana wadanda shugaba Buhari ya zabo da tura sunayen su gaban majalisa a zaman kwararrun jami'an lamuran hajji ne.
Mukaddashin shugaban ya bukaci ba da hadin kai wajen mika ragamar ga sabbin shugabannin hukumar karo na hudu.
Gwamnatin tsohon shugaba Jonathan ta nada Mukhtar gab da lokacin saukar ta daga mulki a 2015.
Mukhtar dai ya zama kwamishinan ayyuka na hukumar tsawon shekaru hudu kafin zama shugaba na tsawon wasu shekaru hudu inda ya kammala wa'adi gabanin aikin hajjin da ya gabata, lamarin da ya sa aka kara masa wasu watanni don jagorantar aikin hajji.
Gyaran sashe na 321 na tsarin mulkin Najeriya na a 2006 ya kafa hukumar alhazan daga da wani sashe na ma'aikatar harkokin waje, inda ministan Abuja na yanzu Muhammad Musa Bello ya zama shugaba na farko har ya kammala wa'adin sa, kana Barista Mukhtar ya samu mukamin daf da saukar shugaba Jonathan a 2015.
Ga karin bayani daga Nasiru Adamu El Hikaya
Your browser doesn’t support HTML5