Hukumomin sun kuma kawar da fargabar cewa ana bada rigakafi mai cutarwa ko kuma wasu hukumomi da basu da izini suna sayar da allurar rigakafin.
Adebimpe Adebiyi, darektan hukumar kula da ayyukan asibitoci, a ma’aikatar kiwon lafiya ta tarayya, ya fitar da wata sanarwa a kan wannan batu.
Sanarwar ta biyo bayan wata wasikar da kwamitin shugaban kasa mai yaki da COVID-19 ya fitar game da gano dubban allurar riga-kafi ta jabu da za a shigo da ita Afirka daga China.
Adebiyi ya ce kafin a iya hana shigowa da riga-kafin jabun, ya kamata ma’aikatar Kwastam ta Najeriya ta kebe filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe a Abuja a matsayin hanya daya tilo da za a rika shiga da allurar rigakafin a Najeriya.
Gwamnati ta ja hankalin darektocin kiwon lafiya a asibitocin tarayya da sauran hukumomin kiwon a kan wannan batun.
Najeriya ta samu zubin riga-kafin miliyan 3.94 na rigakafin Oxford-AstraZeneca, a karkashin shirin tallafin riga-kafi na kasa da kasa na COVAX a farkon watan Maris.