Najeriya Ta Tashi Canjaras Da Rwanda, Za Ta Hadu Da Libya A Watan Oktoba

Tawagar Super Eagles ta Najeriya

Najeriya tana jagorantar rukuni D da maki huɗu, yayin da Rwanda ke matsayi na biyu da maki biyu.

Najeriya ta kasa doke Rwanda a wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Nahiyar Afirka na 2025 da aka buga a Kigali ranar Talata.

An tashi wasan babu ci tsakanin kasashen biyu.

‘Yan wasan na Super Eagles ba su ji dadi, domin an hana su wata kwallo da suka ci a minti na 22.

Victor Boniface ya jefa kwallon ga Ademola Lookman wanda ya zura ta cikin raga, amma alkalin wasa ya hana domin satar gida Lookman ya yi.

Najeriya tana jagorantar rukuni D da maki huɗu, yayin da Rwanda ke matsayi na biyu da maki biyu.

A ranar Asabar Najeriya ta doke Benin a birnin Uyo da ci 3-0.

A watan Oktoba Najeriya za ta kara da Libya a wasanta na gaba.