Babban Bankin Najeriya, (CBN) ya fitar da wani rahoto da ke bayyana yanda tattalin arzikin kasar ya fuskanci koma baya da a kalla kashi 2.27 a cikin watan Agusta, kwatankwacin tafka asarar Naira biliyan 900
A cewar Babban Bankin Najeriya, CBN kudaden shiga da kasar ke samu ya fuskanci koma baya inda ya ragu daga Naira Triliyan 39.57 a cikin watan Yuli zuwa Naira triliyan 38.57 a cikin watan Agusta da ya gabata.
Dakta Isa Abdullahi, kwararren masanin tattalin arzikin kasa ya danganta koma bayan da matsalar cutar COVID-19, da ya yi sanadin dakatar da duk wata hada-hadar kasar a cikin ‘yan watannin da suka gabata.
Wannan matsalar da tattalin arzikin Najeriya ya fuskanta ya samo asali ne daga fuskantar gibi na Naira biliyan 730 na kudaden shigar da gwamnati ke samu daga kamfanoni da kuma bankuna, kwatankwacin faduwar kudaden shigar da gwamnati ke samu daga Naira triliyan 9.5 a watan yuli zuwa Naira triliyan 8.5 a watan Agusta.
Hakazalika rahoton Babban Bankin CBN ya bayyana cewa, shi ma bashin da ake karba daga kamfanoni masu zaman kansu a kasar sun tsaya da wajen Naira triliyan 30.13 a karshen watan Agusta inda ya dan haura da digo 24 idan a ka kwatanta da Naira triliyan 30.06 a watan Yuli.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5