Najeriya Ta Shiga Rukunin Farko a Gasar Cin Kofin CONCACAF

Mexico with CONCACAF 2015 CUP TITLE

Samun nasarar lashe wasan cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru goma sha bakwai na kasashen yammaci, kudanci da tsakiyar Amurka da za’a buga a kakar bana wanda aka fi sani da CONCACAF a takaice, zai zamo wa Amurka da matukar wahala.

Duka kasashen, Amurka da Mexico sun sami kansu a cikin rukunin ‘yan wasan da zai yi wuya su kai labari kamar yadda aka zayyana rukunonin wasan a garin Santiago na kasar Chile, wato babban birnin kasar da za’a gudanar da wasan.

Amurka zata kara da kasar da zata marabci wasan tare da kasar Korosiya da kuma Nageriya duk za su kasance a rukuni guda.

Najeriya ce ke kan gaba, wato ita ke rike da kofin duniya na wasan ‘yan kasa da shekaru goma sha bakwai, kuma sau hudu tana lashe wannan kofi wanda it ace tafi kowace kasa samun nasara a gasar.

“yana da kyau a kowanne lokaci kasan abokin karawar ka domin ka fara shiri da wuri domin fuskantar sa” inji kocin ‘yan wasan kasa da shekaru goma sha bakwai na kasar Amurka a wata hirar sa da wata kafar yada labarai.

“Lokacin farin ciki ne kwarai, kuma a shirye muke mu koma aiki. Chile da Korosiya da Najeriya suna da kwararrun ‘yan wasa kuma kungiyoyin wasan su na da karfin gaske, kuma mun san cewa lallai za’a ji jiki saboda dukkan kungiyoyin masu karfi ne amma mu na da kafrin gwiwa da kuma amince wa ga ‘yan wasan mu. Dan haka muna jiran lokaci ne kawai.

Mexico wadda itace ta ke biye da Najeriya a shekarar 2013, kuma ta lashe gasar a shekarar 2015 inda aka buga wasan a kudancin Amurka, kujma wadda itace ta marabci wasan a shekarar 2011, ta fada cikin gungu na uku wato Group C tare da kasar Australiya , da jamani da Agentina.

Kasar Honduras da Costarica na daga cikin wadanda suka wakilci wasan na CONCACAF na ‘yan kasa da shekaru 17 a gasar, daga 17, ga watan Oktob zuwa 8, ga watan Nuwamba. Honduras na cikin rukunin D tare da Belgium, da Mali da Ecuador. A yayin da Ticos ta zata kasance tare da Afirka ta Kudu da Koria ta Arewa da Rasha duk a rukunini E.