Najeriya Ta Rattaba Hannu Da Rasha Kan Yarjejeniyar Aikin Soja

Prof. Abdullahi Shehu Yibaikwal

Jakadan Najeriya a Rasha, Farfesa Abdullahi Shehu ya bayyana cewa Najeriya da Moscow sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ta shafi sayen kayan aikin soja.

Ofishin Jakadancin Najeriya ya fitar da wata sanarwa da ke cewa yarjejeniyar "ta zayyana tsarin da ya kunshi samar da kayan aikin soji, horar da ma'aikata a cibiyoyin ilimi daban-daban da horon fasaha da dai sauran su."

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito a watan Yuli cewa 'yan majalisar dokokin Amurka sun taka birki kan kudirin sayar da makamai na kusan dala biliyan 1 ga Najeriya saboda damuwar da ke tattare da yiwuwar take hakkin dan adam da gwamnatin kasar ke yi.

Lokacin da aka tambaye shi ko rashin samun irin wannan yarjejeniya da gwamnatin Amurka ne ya yi sanadiyar yarjejeniyar da aka cimma da Rasha, Shehu ya ce a'a.

"Kamar yadda na fada bayan bikin rattaba hannu, na fada a sarari cewa Najeriya ba tana neman wasu hanyoyin na daban ba ne illa na dacewa da moriyar juna," in ji Jakaden Najeriya Farfesa Abdullahi Shehu, a wata hira da Muryar Amurka ta wayar tarho.

"Don Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniya da Rasha ba zai shafi alakarta da hadin gwiwa da manyan abokan huldar ta a duniya ba."

Jakadan na Najeriya ya kara da cewa, "Don haka a gare mu, sanya hannu kan wannan yarjejeniyar, munyi ne don ci gaba da hadin gwiwar da ke tsakaninmu da Tarayyar Rasha a wannan fanni."

Sanarwar ofishin jakadancin ta bayyana yarjejeniyar a matsayin "babban ci gaba" a dangantakar kasashen biyu.

Jakadan Najeriyan yace horon wani bangare ne na yarjejeniyar hadin gwiwar soji tsakanin kasashen biyu.

“Don haka na yi imanin cewa da zaran yarjejeniyar ta fara aiki, kasashen biyu za su tattauna abin da zai zama bukatun Najeriya da yadda Tarayyar Rasha za ta taimaka wa Najeriyar ta wannan hanya,” in ji shi.

Najeriya ta dade tana amfani da wasu jiragen yakin Rasha da jirage masu saukar ungulu, tare da kayan aikin soji da aka saya daga manyan kasashen yamma irin su Amurka, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayan fage, ya fadawa Muryar Amurka a cikin wata sanarwa cewa, "Najeriya babbar aminiya ce a fagen yaki da ta'addanci a Afirka da ƙungiyoyin da ke barazana ga muradun Amurka, tare da mutunta haƙƙin ɗan adam. ”

africa/nigeria-russia-sign-military-agreement