Mutane dake kan hadari ne zasu fara samun maganin da aka yiwa suna Sputnik V, da suka hada da ma’aikatan kiwon lafiya da malaman makaranta. An tabbatar da rigakafin ne a cikin watan Agusta, duk da sukar lamiri da masana daga kasashen yammacin duniya ke yi game da matsalolin dake tattare da gwajin maganin.
Rasha ta shirya bada maganin ne yayin da kamfanonin magani na Amurka da suka hada da Pfizer da BioNTech suke shirin yin haka a mako mai zuwa biyo bayan amincewar kwanan nan da Birtaniya ta yi. Kamfanonin harhada maganin guda biyu, sun samu amincewar Amurka a watan da ya gabata.
Rasha itace kasa ta hudu a duniya da coronavirus tafi barna, inda sama da mutum miliyan biyu da dubu 400 suka kamu da cutar, a cewar cibiyar sa ido a kan cutar ta jami’ar John Hopkins.
A ranar Juma’a, Bahrain ce kasa ta biyu da ta amince da bukatar gaggawa ta amfani da rigakafin coronavirus na kamfanonin Pfizer da BioNTech, baicin Birtaniya.
Kalubalen dake tattare da raba maganin shine ajiye shi cikin yanayi mai sanyi. Dole ne a ajiye magananin cikin sanyin da ya yi kasa da digiri selsos 70. Ita kuwa Bahrain tana samun zafi a duk lokacin rani da ya kai digiri selsos 40.
Tuni Bahrain ta ba mutum dubu shida maganin rigakafin da China ta yi wanda ta yi amfani da matacciyar kwayar cutar. Kasar dake Gabas ta Tsakiya tana da kusan mutum dubu 88 da suka kamu da cutar kana wasu 350 suka mutu a cewar John Hopkins.
Mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a fadin duniya sun haura miliyan 66 kana sama da wasu mutum miliyan guda da dubu 500 ne suka mutu da cutar. Har iyau Amurka itace kan gaba da yawan wadanda suka kamu da cutar da suka kai miliyan 14 da kuma sama da mutum dubu 280 da suka mutu da cutar a cewar John Hopkins.