A yau Litinin Najeriya ta tashi canjarsa da ‘yan wasan Ireland, lamarin da ya ba ta damar zuwa zagayen ‘yan sha-shida ko kuma round of 16 a gasar cin kofin mata ta duniya.
Kungiyar Super Falcons ta zo ta biyu a rukunin B bayan da ta lallasa Australia mai masaukin baki a gasar.
Bayan hutun rabin lokaci ne ‘yan wasan Najeriya suka samu kwarin gwuiwa da fatan zura kwallo a ragar da za ta kai su saman rukunin.
Sauran kiris Najeriya ta zura kwallo, amma mai tsaron ragar Ireland ta doke kwallon, lamarin da ya kai ga wasan ya kare ba tare da kowa ya zura kwallo ba.
Kungiyar Super Falcons wacce ita ce ta 40 a iya taka leda a fagen wasan kwallon kafa na mata a duniya, ba ta sha kaye ko daya ba a wasannin da ta buga, yanzu kuma ta doshi zagayen kwaf-daya.
Ita dai Ireland ta fice a gasar da maki daya kacal.