Binkice na dakin gwaje-gwaje kan lafiyar yara da aka yi kan maganinin Benylin Na Yara ya nuna akwai sinadarin diethylene glycol da yawa, wanda ake dangantawa da mutuwar yara da dama a Gambia, Uzbekistan da Kamaru tun daga shekarar 2022 wanda ke daya daga cikin guba mafi muni a duniya.
Ana amfani da maganin ne wajen magance tari da cututtuka masu nasaba toshewar hanci, zazzabi da sauran matsalolin rashin lafiyar yara masu shekaru biyu zuwa 12, kamar yadda hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC ta fitar a shafinta na yanar gizo.
"Bincike na dakin gwaje-gwaje da aka gudanar a kan samfurin maganin ya nuna cewa ya na ƙunshe da Diethylene glycol fiye da misali kuma an gano cewa yana haifar da mummunar gubar baki ga dabbobin dakin gwaje-gwaje," in ji NAFDAC.
Ya na kuma iya haifar da alamomi kamar ciwon ciki, amai, gudawa, ciwon kai da kuma mummunan rauni na koda wanda zai iya sanadin da mutuwa ga dan Adam, in ji mai kula da lafiyar.
J&J ya bukaci Kenvue (KVUE.N) wanda yanzu shi ne mamallakin maganin Benylin, da ya yi tsokaci game da lamarin.
Kenvue bai amsa nan take ba ga bukatar yin bayanin.