Najeriya Ta Horar Da Dakarun Samanta

Dakarun saman Amurka

Rundunar sojin saman Najeriya, ta gudanar da horo a cibiyar koyar da dabarun ayyukan sojin sama da ke Bauchi.

Horon na musamman ya kunshi daburun yaki, da kuma iya sarrafa kayan yaki ta jirgin sama mai saukar ungulu domin dakile ayyukan ta’addanci da kuma wasu ayyukan bata-gari a fadin kasar.

Bashir Salihu Magashi

Minitsan tsaro Bashir Salihu Magashi ya bayyana gamsuwa da kuma bukatar al’umma su ba da bayanai wa jami’an tsaro domin shawo kan matsalolin tsaro a kasar.

A nasa jawabin, Shugaban Hafsan Sojojin sama na Najeriya, Air Marshall Sadiq Baba Abubakar, ya ce samar da cibiyar horas wa a Bauchi na daga yunkurinsu na kyautata da kuma inganta tsaro idan aka yi la’akkari da matsalolin tsaro da suka addabi yankin Arewa maso gabashi.

Shugaban hafsan sojin saman ya kara da cewa, hada karfi da wasu rukunan jami’an tsaro wuri guda, don a ba su horo kan sabbin dabarun yaki na zamani yana da amfani.

A jawabinsa na rufe taron, Ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihu Magashi mai ritaya, ya yaba da kokarin rundunar sojin saman dangane da horo da ta bai wa jami’anta kan dabarun yaki

Jami’an da aka horar su kimanin 208, ya hada da jami’an 'yan sanda guda goma.

A saurari rahoto cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriyar Ta Horar Da Dakarun Samanta