Yayin da tashe-tashen hankula masu nasaba da tsanar baki ke dada yaduwa a sassan Afirka Ta Kudu, jiya Laraba Najeriya ta yi kira ga ‘yan kasarta da su kauce ma duk wani mataki na ramuwar gayya, bayan da wasu manyan kamfanonin Afirka ta Kudun, akalla biyu, da ke Najeriyar, su ka dakatar da wasu daga cikin harkokinsu saboda hare-haren da aka kai masu.
Ma’aikatar Yada Labaran Najeriya, jiya Laraba, ta fadi ta kafar twitter cewa, “gwamnatin tarayya na kira ga ‘yan Najeriya da kar su kai hari ma kamfanonin Afirka Ta Kudu da ke kasar, a matsayin ramuwar gayyar hare-haren tsana da ake kaiwa kan ‘yan Najeriya a Afurka Ta Kudu.”
Babban kantin nan na ‘yan Afirka Ta Kudu mai suna Shoprite Holdings, ya ce ala tilas ya rufe wasu daga cikin rassan kantin a Afirka Ta Kudun da Najeriya da kuma Zambia bayan hare-haren da aka kai masu, a cewar kafar labarai ta Reuters a jiya Laraba.
Haka zalika, babban kamfanin sadarwar nan na MTN mallakin ‘yan Afirka Ta Kudun, shi ma ya rufe ofisoshinsa da dama a biranen Najeriya, bayan da aka yi ta kai masu hare-hare.