Najeriya ta fara daukan maniyyata hajji zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin bana.
Akalla alhazai kusan 500 aka fara diba daga birnin Abuja da yammacin jiya Lahadi inda mukaddashin shugaban shugaban kasa wanda ya samu wakilcin Ministan Abuja Muhammadu Musa Bello ya bukaci alhazan Najeriya da su zama jakadu na gari.
Ya kuma yi kira ga alhazan da su yi amfani da wannan dama su yi wa kasar addu'a tare da shugaban Muhammadu Buhari da ke jinya.
Da yawa daka cikin maniyyatan sun nuna farin cikinsu da kaddamar da wannan aiki.
“Ba zan iya kayyade iya abinda na ke ji ba, gaskiya ba zan iya ba.” In ji daya daga cikin maniyata hajjin mai suna Usman Adamu.
Babban Malami sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi kira ga maniyyatan da su kasance masu tsoron Allah.
“A can (Saudiya) ba a son kama daura niyyar sabawa Allah, babu inda Musulmi yake alfahri da shi a duniya kamar haka, babu shaidani a cikin garin Makka da Madina, saboda haka sai mu yi kokari mu ga cewa mun tsarkake wannan gari kamar yadda Allah ya tsarkaka shi.” In Sheikh Bala Lau.
Shirin aikin hajjin na bana ya zo da tangarda bayan da hukumomin kasar suka kara kudin zuwa kasa mai tsarki, lamarin da ya sa wasu da dama suka janye zuwa aikin wanda ake yi a shekara-shekara.
Saurari rahoton Nasiru Adamu El Hikaya domin jin cikakken bayani:
Your browser doesn’t support HTML5