Najeriya Ta Fada ciki Komadar Tattalin Arziki

Ministar Kudin Najeriya Kemi Adeosun

Najeriya kasar da tafi kowacce kasa a Afirka bunkasar tattalin arziki ta fada cikin Komadar tattalin Arziki, inda yan kasar ke dandana kudarsu.

Mata da suke saye da sayarwa kasuwa suna wahala sakamakon tashin farashin kayayyakin abinci. Komadar tattalin arzikin ta faru sakamakon abubuwa da yawa, ciki harda hare haren da aka kaiwa kaiwa rijiyoyin man fetur a kudancin kasar, da faduwar farashin danyan man fetur a duniya, da kuma karancin kudaden ketare .

Sannan cire tallafi ko kuma rangwamen da gwamnati ta ke yiwa sayen mai, hakan na sa jigilar kayayyakin noma sukayi tsada.

Rabonda Najeriya ta fada cikin irin wannan yanayi na komadar tattalin arziki yakai shekaru 20 da suka shude, kuma ba’a da tabbacin lokacin da komadar tattalin arzikin zata kare.