A sanarwar da ta fito daga ofishin ministan yada labarun Najeriya Lai Muhammad masu saka jari zasu huta da dogon turancin samun visar
Za'a saukaka lamarin da bukatar bada visar gaggawa daga filayen jiragen sama. Masu saka jari ko yawon shakatawa da bude ido na iya shigowa Najeriya koda kasarsu bata da ofishin jakadancin Najeriya.
Kafin wannan sabon shirin masu aiki a Najeriya ko zuwa taro ko yin wani abu sukan fuskanci wuya kafin su sami visa. Sabbi kuma basu da tabbas.
Hukumar shige da fice ta kara bude ofisoshi 28 a fadin kasar domin saukin samun littafin tafiya, wato, fasfo sanadyar sauya suna ko ga mata da suka yi aure ko kuma bacewar littafin.
Shugaban hukumar shige da fice Muhammadu Baban Dede yace sun horas da ma'aikatansu akan yin anfani da naura mai kwakwalwa ta zamani. Yace sun tsara fasfo din ta yadda babu wani da zai iya wallafa na jabu.
Masana tattakin arziki kan yawan nanata mahimmancin zuwan masu saka jari a kasar a daidai wannan lokacin.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5