Najeriya Ta Bukaci Google Ta Hana Haramtattun Kungiyoyi Amfani Da YouTube

Google Da YouYube

Najeriya ta bukaci Google da ta kawo karshen amfani da kafar YouTube da kafofi na kai tsaye da haramtattun kungiyoyi da kungiyoyin 'yan ta'adda ke yi a kasar, in ji ministan yada labarai Lai Mohammed.

WASHINGTON, D.C. - Najeriya ta yi nazarin hanyoyin da za a bi wajen daidaita yadda ake amfani da shafukan sada zumunta a kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Afirka. Ƙasar tana da miliyoyin masu amfani da intanet da kafafen sada zumunta irinsu YouTube, Twitter (TWTR.N), Facebook (META.O) da Tiktok - wadanda duk sun shahara.

"Kada a bar kafafe da imel da ke kunshe da sunayen kungiyoyin da aka haramta da kuma masu alaka da su a dandalin Google," abin da Mohammed ya ce ya fada wa shugabannin Google a Abuja, babban birnin kasar kenan.

Ministan Yada lLbarai A Najeriya Lai Mohammed

Charles Murito, daraktan Google mai kula da harkokin gwamnati da manufofin jama'a na yankin kudu da hamadar Sahara, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce tuni kamfanin ya tanaji matakan magance matsalolin da gwamnatin Najeriya ke magana a kai.

Wadannan matakan sun haɗa da wani tsari don masu amfani da aka horar da su don nuna abubuwan da ke da matsala, in ji shi. Murito ya ce "Muna da niyya da manufa iri daya." "Ba ma son a yi amfani da dandalinmu wajen aikata munanan ayyuka."

-REUTERS