Najeriya: Shugaba Buhari Ya Karbi Wasu Tsoffin Gwamnoni Biyu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Yanzu babu sauran tababa game da dan takarar gwamnan jihar Bauchi a jam'iyyar APC, jiya shugaba Buhari ya daga hannun gwamna mai ci, yayin kamfe da ya yi a jihar, inda ya karbi wasu jiga jigai daga ja'iyyun adawa cikin su harda tsoffin gwamnoni biyu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sha alwashin zakulo dukiyar kasa daga hannayen mutanen da su ka sace, domin yin aiki ga ‘yan kasa, ya bayyana hakan ne a garin Bauchi, inda ya kai ziyarar wuni guda domin kaddamar da yakin neman zabensa a karo na biyu.

Shugaba Buhari ya karbi jiga jigan ‘yan jam’iyar PDP ta adawa guda goma sha takwas da suka canja sheka zuwa jam’iyar APC mai mulki, wadanda su ka hada da tsoffin gwamnonin jihar Bauchi guda biyu, Ahmed Adamu Mu’azu da kuma Mallam Isa Yuguda.

Sannan kuma ya kara jaddda kudurinsa na ci gaba da kare amanar da ‘yan kasa su ka ba shi.

Wasu ‘yan jam’iyyar ta su ta APC, sun bayyana cewa yanzu haka jam’iyyar ta zamo tungar mutanan da su ka wawure kudaden gwamnati, ganin yadda ake karbar masu canja sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa ta APC.

Wani dan siyasa ya ce daga hannun gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar, da Shugaba Buhari yayi tamkar yayi amaine ya lashe, domin kuwa ada can baya ya na shelar a zabi mutanan da su ka cancanta.

Saurari cikakken rahoto Abdulwahab Muhammad:

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Shugaba Buhari Ya Karbi Wasu Tsoffin Gwamnoni Biyu