Najeriya Sai Tafi Kowace Kasa Cin Gajiyar Taron Rasha

Bayan ganawar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi da shugaban kasar Rasha Vladmir Puting, sun cimma matsaya akan hanyoyin da zasu kara inaganta dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Karamin jakadan Najeriya a Rasha Alhaji Nura Bello Dankade, ya bayyanawa Muryar Amurka abubuwan da aka tattauna da suka hada da inganta harkokin tsaro, samar da layin dogo, da wutar lantarki da dai sauran su.

Kana kuma shugabannin sun rattaba hannu akan wasu yarjejeniyoyi da suka shafi kasuwanci. Gwamnatin Najeriya ta kuma yi kari a kan sunan ma'aikatar sadarwar ta kasar zuwa Sadarwa da Inganta Kasuwanci na Zamani.

Don bukatar karin bayani sai a saurari hirar cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Sai Tafi Kowace Kasa Cin Gajiyar Taron Rasha