Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Bauchi ne ya sanar da cewa rikin ba na addini ba ne, inda ya ce batu ne na soyayya, tsakanin wani saurayi da budurwa.
Da yake jawabi wa al’ummar yankin Yelwa, kwamishinan ‘yan sanda, Umar Mamman Sanda, ya gargadi mazauna Unguwar cewa hukuma ba za ta lamunta da faruwar rikici ba, ya kuma yi karin haske kan abun daya haddasa rikicin.
Shi ma a nasa jawabin, gwamnan jahar Bauchi Bala Abdulkadir Muhammed ya ce rikicin da ke faruwa a yankin wasu ke haddasawa wanda ba ‘yan gurin ba ne ba, kuma dole ne a kamo su, ya kuma bada umurnin da a bude karamin ofishin ‘yan sanda a wurin domin inganta tsaro a yankin.
Hakimin Miri Alhaji Hussaini Abubakar, Dan jikan Bauchi, yayi karatun ta natsu wa mazauna yankin, da kuma karin yin gargadi.
Wani mazaunin yankin wanda rikicin ta shafe shi ya tabbatar cewa rikicin babu addini a ciki, mutane ne suke karkatawa zuwa addini don wata manufa.
Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad:
Your browser doesn’t support HTML5