Najeriya Na Shirin Gwabzawa Da Uruguay

Za a yi karon batta yau asabar a yayin da shahararrun matasa 'yan tamaula na nahiyoyi biyu zasu kece raini a gasar cin kofin 'yan kasa da shekara 17 na duniya
Yau asabar ake shirin karon batta a tsakanin gwanayen tamaula na nahiyoyi biyu a ci gaba da gasar cin kofin duniya na samari 'yan kasa da shekara 17 a Hadaddiyar Daular Larabawa, inda Najeriya zata gwabza da Uruguay, ita kuma Cote D'Ivoure zata kara da Argentina.

Cote D'Ivoire da Argentina su zasu fara karawa a Sharjah da karfe 6 na maraice.

Daga cikin kasashen hudun da suke wasa a yau, Najeriya ce kawai ta taba lashe wannan kofin. Ba ma sau daya ko biyu ba, har sau uku. Amma zasu fuskanci kalubale daga 'yan wasan Uruguay, wadanda a cikin 'yan shekarun nan suka fara nuna kwazo sosai a wannan gasa.

Masana kwallon kafa da dama su na nuni da cewa irin takawar da Najeriya ta yi a wannan gasa a bana, ta sa ana ganin da gaske tana sahun gaba cikin wadanda suka fi kwadayin daukar wannan kofi.

A karshen zagaye na biyu na wannan gasa, Najeriya tana kan gaba, tare da kasar Brazil, a zaman wadanda suka fi jefa kwallaye a raga, inda Najeriyar ta zura kwallaye 18 a wasanni 4 da ta yi. A zagayen na biyu, Najeriya ta doke Iran da ci 4-1.

Sai dai ana ganin, kasar Uruguay ma ba kanwar lasa ba ce.