Najeriya Na Samar Da Lantarkin Sa’o’i 24 Ga Togo, Nijar, Jamhuriyar Benin -  TCN

Electricity pylons of high-voltage electrical power lines in Bouchain

A makon daya gabata bangaren lantarkin Najeriya ya gamu da jerin tankardar daukewar wuta inda babban layin samarda lantarkin na kasar ya ruguje har sau 3 a cikin kwanaki 7.

Kamfanin samar da hasken lantarki na Najeriya (TCN) yace kasar na samar da lantarki ga kasashen makwabtanta irinsu Togo da Benin da Jamhuriyar Nijar.

Shugaban tcn Sule Abdulaziz ne ya bayyana hakan a shirin siyasar tashar talabijin ta Channels na jiya Lahadi “Sunday Politics”.

“Mu ke samar wa kasashen Togo da Benin da Jamhuriyar Nijar da hasken lantarki,” a cewar sa a cikin shirin.

“Kwarai, suna samun lantarki daga Najeriya tsawon sa’o’i 24 kuma suna biya,” inji shugaban na TCN.

A makon daya gabata bangaren lantarkin Najeriya ya gamu da jerin tankardar daukewar wuta inda babban layin samarda lantarkin na kasar ya ruguje har sau 3 a cikin kwanaki 7.

Sai dai Abdulaziz ya bayyana cewar wasu ‘yan Najeriya na samun lantarkin babu daukewa musamman wadanda ke kan damarar “A”.

“Wasu ‘yan Najeriya na samun wuta tsawon sa’o’i 24; amma fa ba kowa ba. Za’a ga suna samun wutar tsawon sa’o’i 20 zuwa 22, sune wadanda ke kan damarar a,” a cewarsa.

A cewar, kamfanonin rarraba hasken lantarki (DISCOS) sun fi bada fifiko ga abokan huldarsu dake kan damarar “A” kuma ana sa ran su samar musu da wuta ta tsakanin sa’o’i 18 zuwa 22.”

Yawan rushewar babban layin lantarkin na kasa ya janyo damuwa tsakanin ‘yan Najeriyar da tuhumar yadda ake gudanar da bangaren lantarkin kasar.

Sai dai, shugaban na TCN ya dora alhakin yawan lalacewar layin wutar a kan tsofan da kayayyakin suka yi sannan ya bada tabbacin cewa ana kokarin samar da wani layin da zai tallafa wancan.