Masara na daya daga cikin kayayyakin masarufi da al’umma Afirka suka fi dogaro akai wajen ciyar da al’umma da bunkasa tattalin arzikinsu ciki har da Najeriya.
Sai dai shekarar da ta gabata an dan fuskanci matsi sakamokon annobar Covid-19 da matsaloli irin na ayyukan ta’addaci da ambaliyar ruwan sama da dai sauransu wadanda suka yi sanadiyar hana manoma zuwa gonaki don gudanar da ayyukansu.
Amma a wannan shekara ta 2021 shugaban kungiyar manoma da masu sarrafa masarar da sayar da ita Dakta Abubakar-Annur Bello Funtua ya bayyana cewa Najeriya na da isasshen masarar da za ta wadaci al’umma kasar.
Hakan ya sa wasu manoma kamar Mallam Islama’il jibya, sun bayyana farin ciki dangane da wannan sanarwa.
Daga Cikin ayyukan da kungiyar ta manoma da masu sarrafa masara da sayar da ita a Najeria ta sa a gaba shi ne hada kai don cika burin gwamnati na ganin an wadata kasa da abinci kamar yanda shugaban ya yi kari akai.
A saurari rahoto cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim:
Your browser doesn’t support HTML5