Najeriya ce ta uku a jerin kasashe mafiya samar da citta a duniya bayan Indiya da China, kuma annobar COVID-19 ba ta shafi cikinta ba, saboda magungunan da ake bukata wajen wannan saiwa mai yaji.
To amma manoman Najeriya, wadanda ke amfani da wasu dabarun noma irin na da, na ta fama wajen ganin sun amfana.
Wannan shekarar, wani manomin citta mai suna Shedrack Nyumo, na shuka hatsi ganga da cittarsa saboda ya cike gibin asara mai yawa da ya yi cikin shekaru biyu da su ka gabata, lokacin da farashin citta ya fadi da wajen kashi 80%.
To amma yayin da masu sayan citta a duniya ke ta kokarin amfana da magungunan da ake ganin ta na dauke da su a wannan marra ta annobar corona, farashinta na karuwa kuma masu saye na karuwa. Hasali ma, yanzu Nyumo na yin da-na-sanin rashin shuka citta fiye da haka.
Manomin citta, Nyumo ya ce da a ce ya san cewa farashin citta zai karu haka, da ya shuka kadada fiye ma da dari biyu, ya ce kadada 80 ne kawai ya shuka a wannan shekarar saboda asarar da ya yi a baya.
Nyumo dai ya fito ne daga kauyen Kwoi na Kudancin jahar Kaduna ta arewa maso gabashin Najeriya. Wannan yankin ya yi fice wajen noman citta.
Da dama daga cikin mazuna wannan yankin manoman citta ne, kuma fiye da kashi 50 cikin dari na cittar da Najeriya ke samarwa a nan ake nomawa. To amma da dama daga cikin manoman cittar, na amfani ne da dabaru marasa inganci da kan jawo masu kashe kudi sosai.
Don haka, kodayake farashin kilogiram 40 na buhun citta ya ninka har sau hudu a wannan shekarar, wato daga dala 20 zuwa wajen dala 83, manoman basu ganin ribar ba sosai.
Wani manomin kuma mai suna Jamilu Jibril ya ce, “manoma na bukatar karin kayan aiki, gwamnati ta yi kokari amma mu na bukatar karin kayan aikin gona – kamar na’urorin tsagawa da yankewa da kuma busarwa, wadda za ta busar ta kuma tsaftace cittar Najeriya ta yadda za ta samu karbuwa a kasashen waje.”
Abdulbashir Abubakar, Sakatare-Janar na kungiyar Manoma Da Masu Sayar Da Citta, ya ce akwai kwararru kan harkokin noma da yawa da kan zagaya su na ilimantar da manoman karkara kan dabarun noma, da yadda ake kashe kwari, da kuma yadda ake zuba taki da dai sauransu, ta yadda amfanin gonakinsu za su yi daraja a kasuwanni.
Timothy Obiezu ne ya hada wannan rahoton