Najeriya na bin kamfanin man fetur NNPC dala biliyan ashirin da biyar

Ibe Kachikwu shugaban NNPC kuma karamin ministan man fetur na Najeriya

Tsakanin shekarar 2011 zuwa shekarar 2015 kamfanin NNPC ya rike dala biliyan ashirin da biyar cikin kudin man fetur da ya sayar amma bai saka cikin baitulmalin gwamnati ba.

Gwamnatin Najeriya na bin kamfanin NNPC dala biliyan 25 kudin dayan man da aka sayar da kamfanin bai saka cikin asusun gwamnati ba.

Kwamitin dake sa ido akan kudaden gwamnati da ake kira RMAFC a takaice ya sanarda hakan .

Mai magana da yawun kwamitin Ibrahim Muhammad shi ya fada shekaranjiya Litinin. Yace kudin na danyen man da aka sayar ne tsakanin shekarar 2011 zuwa shekara ta 2015.

A nahiyar Afirka Najeriya ce ta fi kowace kasa arzikin man fetur.

Kamar yadda OPEC ta sanar kowace shekara Najeriya na samun kudi kimanin dala biliyan 77 daga sayar da man fetur kawai.. Amma duk da wannan arzikin wajen kashi 66 cikin 100 na 'yan kasar ke fama da talauci lamarin da ya sa mutane suke zaton cin hanci da rashawa sun yiw kasar katutu musamman a kamfanin NNPC na kasar