Najeriya: Matakin Buhari Na Dakatar Da Jami'an Gwamnati

Wasu yan rajin yaki da cin hanci da rashawa sun ce matakin da shugaban kasa ya dauka na dakatar da wasu manyan jami’ansa biyu yakamata a kara dauka.

A shekaranjiya Laraba ne shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta kasa Cif Ayo Oke da aka alankantashi da makudan kudade da suka kai sama da dala miliyon 40 da hukumar EFCC ta kama a wani gida a birnin Lagos da kuma sakataren gwamnati David Babachir Lawal, wanda ake zarginsa da karbar rashawa a wata kwangila.


Abdulkarim Dayyabu shine shugaban wata kungiya mai zaman kanta ta Movement for Justice kuma yace matakin dakatar manyan jami’an ya zo a makare.


Da yakje ci gaba da hira da sashen Hausa na Muryar Amurka a jiya Alhamis, Abdulkarim yace wannan wani mataki ne da yakamata a ce an dauka da dadewa. Yace yakamata ace shugaba Buhari ya dau mataki a kan duk wanda aka same shi da karban rashawa ba sai an jira lokaci mai tsawo ba.


Shima Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda mamba ne na jami’iyar APC mai mulki wanda ya baiwa shugaba shawarar daukar matakai a kan sauran mataimakansa.

Ya ce a karshe dai shugaba Buhari na yaki da rashawa a cikin gida. Yace shugaban ya ci gaba da sa ido kan jami’an gwamnatinsa, musamman manyan jami’ansa wanda ake zarginsu da rashawa.

Ita ma Naja’atu Mohammed ta yi taka tsantsan a bayaninta tana cewar jami’an da aka dakatar da su din zasu yi bayani, tace a baya gwamnati ta kare Lawal a lokacin da majalisar dattawa ta tuhumeshi da karbar rashawa.