Jihar Neja na ‘daya daga cikin jihohin Najeriya da aka samu asarar rayuka sakamakon barkewar cutar Sankarau, da ake samu ta hanyar kwana cikin zafi da cunkoson jama’a.
A wani taron manema labarai daraktan kula da lafiyar jama’a na ma’aikatar lafiyar jihar Neja, Dakta Usman Mohammed, yace yanzu haka suna gudanar da bincike akan labarin da suka samu na sayar da maganin rigakafin cutar Sankarau, da gwamnati ke baiwa jama’a kyauta.
Kawo yanzu dai an tabbatar da cewa mutane 33 cutar ta kashe a jihar Neja, haka kuma an sami mutane 123 dauke da cutar a cewar Dakta Usman Mohammad.
Sai dai kuma cutar Sankarau ta fi yin tsanani a jihohin Zamfara da Sokoto da kuma Kebbi. Hakan yasa jihohin ke hada hannu domin samun hanyar shawo kan cutar.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum