Najeriya: Kungiyoyin Fararen Hula Sun Fitar Da Kundayen Yaki Da Cin Hanci

A Najeriya wasu kungiyoyin fararen hula tare da hadin gwiwa da gidauniyar MacArthur Foundation ta kasar Amurka, sun kaddamar da wasu kundaye da ke dauke da rahotanni da 'yan jaridar kasar suka wallafa wajen fahimtar da al'umma.

Kundayen guda biyu na dauke da rahotanni ne da 'yan jarida a Najeriya suka wallafa daga shekara 2017 zuwa 2018, wadanda suka hada da yadda hukumomin yaki da cin hanci da rashawa irin su EFCC da ICPC suka gudanar da ayyukansu a wadannan shekarun.

Dan Jarida Musa Adamu, ya nuna damuwarsa a kan yadda ire -iren wadanan rahotannin ba sa yin tasiri, domin a cewar shi, mahukunta ba sa daukan rahotanni da muhimmanci, amma kuma 'yan jaridar za su ci gaba da aikinsu.

Shugaban kungiyar CISLAC masu sa ido a harkar ayyukan majalisu, Auwal Musa Rafsanjani, ya ce, burinsu shi ne, majalisa da hukumomin gwamnati, su yi amfani da kundayen wajen yin nazari a ayyukansu na sa ido a yadda ake sarrafa kudaden al'umma.

Shi ma Alhaji Aminu Majidadi, shugaban kungiyar Almushahid, masu fashin baki a harkokin cin hanci da rashawa, ya ce burinsu shi ne ganin yadda mahukuntan za su mayar da hankali wajen hukunta duk wanda aka samu da laifin cin hanci ko yin sama da fadi da kudaden jama'a.

Abin jira a gani shi ne ko wadannan kundaye za su sha banban da wadanda suka gabata wajen taimakawa hukumomin domin samun nasarar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Ga cikakken rahotun daga wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Kungiyoyin Fararen Hula Sun Fitar Da Kundayen Yaki Da Cin Hanci